23 Yuli 2026 - 14:51
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Sake Buɗe Wuraren Fakewa A Tel Avil Saboda Tsoron Makaman Iran

Sake buɗe matsugunan da ke kewayen Tel Aviv yana zuwa ne saboda takatsantsan da tsoron makamai masu linzami na Iran inda shirin hakan ya kankama a Isra'ila 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Magajin garin Ramat Gan, da ke kewayen Tel Aviv, ya ba da labarin sake buɗe matsugunan jama'a na garin, kuma ya jaddada cewa wannan mataki an ɗauke shi ne kawai don yin taka-tsantsan.

Carmel Shama HaCohen a shafinsa na Facebook ya sanar da cewa " a bisa kimantawa sun nuna cewa haɗarin hare-haren makamai masu linzami daga Iran a ƙarshen mako ya ƙaru, kuma ba za a iya ɗaukar shi a matsayin ƙaramin abu ba." Wannan jami'in Isra'ila ya kuma bukaci manajojin gine-ginen zama da su sake buɗe matsugunan gama-gari na gine-ginen da ake fakewa yayin Hare-haren.

.....

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha